Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sallami dan Mataimakin Shugaban Amurka Daga Soja


Mataimakin shugaban Amurka, Joe Biden.
Mataimakin shugaban Amurka, Joe Biden.

An kori dan gidan mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden daga rundunar sojan Amurka.

An kori dan gidan mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden daga rundunar sojan Amurka, bayanda wani gwajin da aka yi mishi ya nuna cewa yayi amfani da garin hodar iblis ta cocaine.

Rahottanin kafofin watsa labarai da suka fito a yau Alhamis sun ce shi Hunter Biden ya fa’di wani gwajin kwayoyin da’akayi tun watan yuni na shekarar data wuce.

Rundunar sojin ruwa da shi dan mataimakin shugaban kasar yake aiki, ta tabbatar da korar kuma sunce ya farune tun watan Fabarairu, amma sunki bada dalili.

A wani bayani shi dan shekara 44 da haihuwa yanuna damuwarsa dakuma jin kunyarsa kan abinda da ya aikata, kuma ya darajanta hukuncin da rundunar sojan ta yanke masa.

Ofishin mahaifinsa wato mataimakin shugaban kasa, haryanzu dai bai yi wani bayani ba akan korar, wadda gidan jaridar Wall Street Journal ne ta fara wallafa labarin.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG