Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sako Tagwayen Da Yan Bindiga Su Ka Sace a Zamfara


An sako tagwayen da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Zamfara, bayan da aka biya su kudin fansa.

Rahotanni daga jihar Zamfara a Najeriya na cewa da yammacin jiya Asabar masu garkuwa da mutane sun sako ‘yan matan nan tagwaye da suka sace tun watan jiya.

An sako Hasana da Usaina ne bayan da aka biya kudin fansa da adadinsu ya kai Naira Miliyan 15, da aka samu tarawa da taimakon wasu dai dai kun jama’a, harma da ‘yan siyasa a ciki da wajen jihar Zamfara.

Sai dai an sako tagwayen ne kadai ba tare da ‘yar uwarsu Sumaiya ba, wacce aka sace su tare a gidan aurenta a garin Dauren.

Wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka, Murtala Faruk Sanyinna ya zanta da daya daga cikin ‘yan uwan yaran, Abubakar Muhammad Zurmi.

Domin karin bayani saurari rahotan Murtala Faruk Sanyinna.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG