Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta yi na’am da yadda bangarorin rikicin Libya suka nuna amincewa soma tantaunawa da junansu a karkashin shiga tsakanin kasar Faransa don fitarda wannan kasa daga halin wargajewar da ta tsinci kanta ciki bayan faduwar gwamnatin Gaddafi,
Ministan harakokin wajen Nijar Ibrahim Yabuba ne ya bayana haka.a hirarsa da wakilin muryar Amurka Sule Mumuni Barma, a Yamai, ya ce za a ci nasarar abinda aka sa a gaba idan manyan kasashe su kayi abinda ya dace da gaske.
Ya ce an jima ana batun samun zaman lafiya a Libiya amma saboda babu gaskiya yasa lamari ya kawo yanzu, yana mai cewa idan har ana bukatar samun nasara sai an bar ‘yan Libya suyi tsarinsu da kansu da guddanar da zabe domin zaben shugaban da suke so wanda kuma kowa ya yarda dashi.
Ministan ya kara da cewa kasashe da dama suna ciki Libya da jami’an su da ikirarin son taimakawa Libya, amma kuma da wani tsari na manufarsu a boye dangane da arzikin Libya, amma ga kasar Nijar, in ji Ministan babu wannan manufar illa son samun zaman lafiya domin samun ci gaba da kwanciyar hankalin a Libya da kasashe makwabtanta.
Facebook Forum