Da can baya kauyukan Ibi sun sha fama da samun hare-hare daga kabilar Tarok na jihar Filato da suke makwaftaka da su. Wannan sabon harin da aka kai kauyen Tabga ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da goma da kuma wasu goma da suka jikata. Yanzu ana yi masu jinya a asibitin gwamnati. Amma akwai wasu fiye da hamsin da ba'a san inda suke ba. Tuni dai aka kai jami'an tsaro.
Ishaku Adamu shugaban karamar hukumar Ibi ya tabbatar da cewa mutane ne daga jihar Filato wadanda suka saba tare hanya musamman ranar kasuwa domin su yiwa mutane fashi.Ya ce sun dade suna yin hakan to amma yanzu abun ya dauki wani sabon salo inda sun soma kai hari cikin kauyuka, suna bi suna kashe mutane. Yawancin mutanen dake Tabga sun gudu daga gidajensu zuwa cikin garin Ibi. Wasu sun tsere zuwa Wukari domin tsoron hare-haren da kabilar Tarok ke kai masu.
Karamar hukumar, a ta bakin shugabanta Ishakau Adamu ta samarda makarantu uku inda ta shugunar da wadanda basu da wurin da zasu fake. Sun taimakesu da magani da abinci da dai makamantansu. Yanzu dai 'yan sanda suna nan suna shawagi a kauyen dama wasu wuraren domin tabbatar da zaman lafiya. Shi kuma mukkadashin gwamnan jihar Taraba ya ce zasu dauki kwararan matakai kuma zasu kwakulo duk wadanda suke da hannu wurin kai hare-haren.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.