Matsalar satar mutane domin neman kudin fansa dai na cikin matsalolin tsaron dake addabar jama’a yanzu, inda akan sace mutane tare da neman kudin fansa.
‘Dan majalisar da aka sace Hon. Hosea Ibi, shi ke wakiltar mazabar Takum ta daya a majalisar dokokin jihar Taraba, wanda kuma kawo yanzu ba’a san inda aka yi da shi ba, kuma wannan lamari ya jefa al’ummar yankin cikin zulumi.
Bayanai na nuni da cewa an sace ‘dan majalisar ne a gidan mahaifiyarsa cikin dare lokacin da ya je duba ta, kuma suna cikin hira da mahaifiyar ne sai wasu yan bindiga uku, dauke da manyan bindigogi suka yi dirar mikiya suka kwace wayoyin mutanen gidan, kafin daga bisani suka iza keyarsa zuwa kan wani mashin suka yi awon gaba dashi. Kawo yanzu dai ba a san halin da dan majalisar yake ciki ba, kamar yadda wani mazaunin yankin ya tabbatar.
Rundunar yan sandan jihar Taraba ta tabbatar da faruwar lamarin, inda kakakin rundunan David Misal ya ce, tuni aka baza kwararrun jami’ai da kuma yan shirin ko ta kwana don ceto dan majalisar da aka sace.
Jihar Taraba dai ta yi kaurin suna wajen wannan matsalar na satar mutane domin neman kudin fansa.
Facebook Forum