Rahotanni daga Botswana na cewa, masu kada kuri’a sun kai har yammacin jiya Laraba suna bin dogon layi domin su jefa kuri’unsu, duk ko da cewa an rufe rumfunan zabe.
Hukumar zaben kasar ta ce, ta ba mutanen da suka riga suka shiga dakunan jefa kuri’a damar jefa kuri’unsu, amma wadanda ba su kai ga shiga dakunan ba, an dakatar da su daga kofa.
“Ban jima da kada kuri’ata ba, ina so na nuna gamsuwata kan yadda aka tsara komai, layuka sun yi tsayi, amma dai an yi komai cikin lumana.” Inji wata matashiya mai suna Siboneni Phepheng, wacce wannan shi ne karon farko da ta kada kuri’a zaben kasar ta Botswana.
Nan dai da kwanaki biyu ake sa ran hukumar zaben kasar ta IEC za ta bayyana sakamakon zaben, wanda aka kara tsakanin Shugaba mai ci Mokgweetsi Masisi na jam’iyyar BDP da abokin hamayyarsa Duma Boko na jam’iyyar adawa ta UDC.
Facebook Forum