El-Sissi ya yi rantsuwar kama aiki a gaban majalisar dokokin kasar, wadda ta yi taro a sabuwar hedkwatar gudanarwa a cikin hamadar da ke wajen birnin Alkahira.
El-Sissi ya lashe kashi 89.6% na kuri'un da aka kada a zaben na Disamba, inda kashi 66.8% suka kada kuri'a sama da miliyan 67 da suka yi rajista. Ya yi takara da ’yan adawa uku da ba a ma san su ba.
Yaƙin Isra'ila da Hamas a Gaza da ke kan iyakar gabashin Masar ne ya danne zancen zaben wanda yaki ne da ya yi barazanar faɗaɗa a yankin.
An fara zaben El-Sissi ne a matsayin shugaban kasa a tsakiyar shekara ta 2014, sannan aka sake zabensa a shekara ta 2018. Bayan shekara guda, sauye-sauyen kundin tsarin mulkin kasar, a kuri'ar jin ra'ayin jama'a, ya sa shi ya kara shekaru biyu a wa'adi na biyu kuma ya ba shi damar tsayawa takara karo na uku mai wa'adin shekaru shida.
Tun dama mutane da yawa na ganin ba makawa sai ya yi nasara a wannan zabe na baya bayan nan. Abokan hamayyarsa guda uku ’yan siyasa ne marasa rinjaye wadanda ba kasafai ake ganin su ba a lokacin yakin neman zabe.
Dandalin Mu Tattauna