An rantsar da mukaddashin gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa a matsayin gwamnan jihar.
An gudanar da rantsuwar ne a dakin taro na Cocoa da ke ofishin gwamna a Akure, babban birnin jihar, wanda Babban Alkalin Kotun, Mai shari’a Olusegun Odusola ya gudanar da karfe 5:18 na yamma.
Tsohon Gwamna, Oluwarotimi Akeredolu, mai shekaru 67,ya rasu ne a ranar Laraba, 27 ga watan Disamba, an ce ya mutu ne sakamakon cutar sankarar jini mai suna “Leukemia”.
Gwamnan ya bar mata mai suna Betty Anyanwu-Akeredolu da ‘ya’ya hudu.
Dandalin Mu Tattauna