Gwamnatin mulkin sojin kasar Burkina Faso ta nada tsohon ministan sadarwa Rimtalba Jean Emmanuel Ouedraogo a matsayin firaministan kasar a jiya Assabar, kamar yadda wata dokar soja ta bayyana, kwana guda bayan rusa gwamnati.
Ouedraogo ya yi aiki a majalisar ministocin firaminista mai barin gado, Apollinaire Joachim Kelem de Tambela, wanda Kyaftin Ibrahim Traore ya cire daga mukaminsa a ranar Juma'a.
Ba’a bayyana dalilin korar Tambela ba, wanda ya jagoranci gwamnatoci uku da sojoji suka nada tun bayan da Traore ya hau karagar mulki a shekara ta 2022.
Ouedraogo wanda babban makusancin Traore ne kuma dan jarida, ya taba zama babban edita da kuma darektan gidan talabijin na Sahel na kasar.
Bayan juyin mulkin watan Satumban shekara ta 2022, Traore ya zabi Ouedraogo a matsayin Ministan Sadarwa kuma mai magana da yawun gwamnati a matsayin farar hula a cikin gwamnatin ta soja.
Kasar da ke yammacin Afirka ta fada cikin rashin kwanciyar hankali sakamakon juyin mulkin watan Janairun 2022 inda Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba ya kwace mulki.
Bayan fiye da watanni takwas, Traore, mai shekaru 36, wanda yanzu ke jagorantar gwamnatin mulkin soja ya hambare Damiba.
Dandalin Mu Tattauna