Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Mika Wata ‘Yar Najeriya Ga Hukumomin Italiya Bayan Samun Ta Da Laifi A Harkar Karuwanci 


Hukumomin Najeriya sun mika wata ‘yar kasar da ake nema ruwa a jallo ga hukumomin Italiya wacce tun a shekarar 2010 ake nema ruwa a jallo, bayan hukuncin daurin shekaru 13 da aka yanke mata a Italiyar.

WASHINGTON, D.C. - An tuhumi Joy Jeff mai shekaru 48, wacce fitacciya ce a kungiyar ‘yan mafiya a Najeriya da laifin gudanar da wani gungun da ya shahara wajen ayyukan karuwanci a Italiya.

Wata yarjejeniya da ke tsakain kasar Italiya da Najeriya ce ta ba da damar kama ta.

Wata sanarwa ta ce an kama ta ne a Najeriyar a ranar 4 ga watan Yunin 2022 a Najeriya bisa sammacin kasa da kasa da kasar Italiya ta ayyana.

Masu bincike na Italiya a birnin Ancona da ke gabashin kasar sun ce Jeff ta taka rawa wajen safarar mata zuwa Italiya, Sifaniya da Netherlands, inda aka tilasta musu yin karuwanci ta hanyar cin zarafi da barazana. An yanke mata hukunci tun ba ta nan.

Wani faifan bidiyon da ‘yan sandan kasar Italiya suka fitar ya nuna yadda aka dauko matar daga Abuja babban birnin Najeriya zuwa filin jirgin Ciampino da ke Rome inda ‘yan sanda suka dauke ta a keken guragu.

-Reuters

XS
SM
MD
LG