Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kori Ma'aikatan Gidan Talabijin Sakamakon Yajin Aiki A Nijar


Canal 3 Nijar
Canal 3 Nijar

A jamhuriyar Nijar wani gidan talabijan mai zaman kansa wato Canal 3 Nijar ya kori ma’aikata sama da 30 bayan da suka tsunduma yajin aikin kwanaki 3 a makon da ya gabata.

Ma’aikatan na korafi ne akan rashin samun albashi na tsawon watanni a kalla 15. mafarin kenan suka jingine aiki.

Daya daga cikin ma'aikatan farko farko na gidan talabijin din, wadda ta shafe shekara 16 tana aiki da Canal 3 Nijar, Hajia Salamatou Maidaji, ta ce da ita da abokan aikinta sun sha alwashin kai kara ga hukumomi domin samun hakkokinsu.

Domin jin martanin shugabanin kafar, Muryar Amurka ta tuntubi shugaban ma’aikata DRH Amadou Tidjani Alhaji Anis amma ya ce ba zasu ce komai ba a game da al’amarin.

Sakataren Kungiyar kare hakkin ma’aikatan kafafen labarai ta SYNATIC Moudi Moussa wanda ya fara tuntubar ma’aikatan Canal 3 da shugabanin tashar don samar da maslaha na cewa lokaci ya yi da za a dubi irin wannan matsala da idon rahama.

Annobar cutar corona da aka fuskanta daga 2019 zuwa 2020 ta matukar tagayyarar da kafafe masu zaman kansu a Nijar, inda biyan haya da wutar lantarki da haraji ke masu wuya kafin daga bisani biyan albashi ya fara zama jidali.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG