Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kona Ofishin Jam'iyyar APC A Kano


'Yan daba sun kona ofishin APC a Kano.
'Yan daba sun kona ofishin APC a Kano.

Wannan lamari na zuwa ne kwana 2 bayan da wata babbar kotu a Abuja ta tabbatar da shugabannin jam’iyyar ta APC da aka zaba daga bangaren Sha’aban Sharada da Malam Shekarau, a zaman halatattun zababbin shugabannin APC.

Wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun kai farmaki tare da kona ofishin shelkwatar jam’iyyar APC na jihar Kano.

An kona ofishin wanda ke kan titin Maiduguri a cikin birnin Kano, na bangaren tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau da safiyar yau Alhamis, kuma ana zargin ‘yan dabar sun fito ne daga bangaren jam’iyyar ta APC da ke adawa da bangaren na Shekarau.

'Yan daba sun kona ofishin APC a Kano
'Yan daba sun kona ofishin APC a Kano

Wannan lamari dai na zuwa ne kwana 2 bayan da wata babbar kotu a Abuja ta tabbatar da shugabannin jam’iyyar ta APC da aka zaba daga bangaren na Sha’aban Sharada da Malam Shekarau, a zaman halatattun zababbin shugabanni, inda kuma ta rusa zaben da bangaren gwamna Abullahi Umar Ganduje suka gudanar.

A cikin hukuncin na kotun, mai shari’a Hamzat Muazu ya ba da umarnin hannunta musu dukkan lamurran shugabancin jam’iyyar.

Idan za’a iya tunawa a ranar 31 ga watan Yulin wannan shekara ne bangaren jam’iyyar APC na gwamna Ganduje ya ba da sanarwar dukkan ‘yan takarar shugabancin jam’iyyar da suke daga bangarensu, da cewa su ne halatattun shugabanni da aka zaba ta hanyar sasantawa.

To sai dai kuma Sharada ya garzaya kotu, inda ya kalubalanci wannan sanarwa, bayan da su ma sun gudanar da zabe a na su bangare.

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG