Masu fafutukar auren jinsi, luwadi da madigo a Najeriya na bayyana damuwa kan tsaron lafiyarsu, bayan da aka kashe wani fitaccen dan daudu da aka fi sani da “Abuja Area Mama”, a Abuja babban birnin kasar.
An tsinci gawar "Area Mama" a bakin titi a ranar Alhamis, kuma abokinsa Franklin Ejiogu ya ce ba a san yadda lamarin ya faru ba, amma an ga raunin harbin bindiga a kansa.
Ejiogu ya dora alhakin yawaitar hare-hare da ake kaiwa kan masu luwadi da madigo da auren jinsi a Najeriya, da sanya hannu kan yarjejeniyar na ta Samoa da gwamnatin kasar ta yi.
Hukumomin na Najeriya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar Samoa mai cike da cece-kuce, wata yarjejeniya tsakanin kungiyar Tarayyar Turai ta EU da wasu kasashe 79 da suka hada da kasashen nahiyar Afirka, Caribbean da Pacific, a ranar 28 ga watan Yuni.
Gwamnatin kasar ta ce yarjejeniyar na da nufin karfafa hadin gwiwa kan ka'idojin dimokaradiyya da kare hakkin bil'adama tare da inganta ci gaban tattalin arziki da ci gaba.
Sai dai masu suka, ciki har da 'yan majalisar dokokin kasar, sun ce akwai bukatar a kara bayyana yarjejeniyar kan wasu sharuddan da ke karfafa 'yancin jinsi.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kaddamar da bincike kan kisan na Area Mama. To sai dai kuma kakakin rundunar ‘yan sandan a Abuja, Josephine Adeh, ba ta amsa bukatar tattaunawa da Muryar Amurka ba.
Sai dai mai fafutukar LGBTQ+, Promise Ohiri, wanda aka fi sani da Empress Cookie, ya ce irin wannan kisan, idan ba a hukunta shi ba, zai kara karfafa laifukan nuna kyama.
Dokar kasa ta Najeriya ta yi tanadin hukuncin daurin shekaru 14 a kan auren jinsi. Kuma a yankin arewacin kasar da ke da rinjayen Musulmi, zai iya kai wa ga yanke hukuncin kisa a karkashin dokokin Shari'a.
Dandalin Mu Tattauna