Wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda Biu ya garzaya inda wannan abu ya faru, inda aka zube gawarwaki na mata da maza da yara a kasa. Wasu daga cikin wadanda suka mutu yanka su akayi, wasu kuma aka harbe su da bindiga, wasu kuma aka kona su da wuta.
An jere gawarwakin ne a babban Masallacin garin, su wajen 39, sannan suka kona kaso 75 cikin dari na gidajen garin baki daya.
‘Yan bindigan suna kasuwanni, da asibitoci da kuma ma’aikatu.
A halin yanzu dai, tarzomar ta lafa, inda aka kai jami’an tsaro wannan gari domin tabbatar da zaman lafiya, sannan gwamnati tayi alkawarin cewa zata kai tallafin kayan agaji ga mutanen da wannan lamari ya shafa.
A halin yanzu dai, mata da yara da yawa a cikin wannan gari suna zaune ne a karkashin bishiyoyi.