Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kammala Bukin Makon Hakar Ma'adinai Ta Najeriya


Ma'aikata a mahakar ma'adanai suna sarafa zinari a kauyen Anka a jihar Zamfara arewa maso yammacin Najeriya.
Ma'aikata a mahakar ma'adanai suna sarafa zinari a kauyen Anka a jihar Zamfara arewa maso yammacin Najeriya.

Najeriya ta karbi bakuncin taron hako ma'adinai na shekara-shekara a babban birnin kasar cikin wannan makon domin tattauna hanyoyin zuba jari da matakan da ake bukata don bunkasa fannin.

Najeriya ta kammala wani taro na kwanaki uku domin bikin makon ma'adinai na kasa.

Mahukunta a yammacin Afirka na neman fadada zuba jari a masana'antar hakar ma'adinai a wani yunkuri na daidaita tattalin arziki, a daidai lokacin da ake fama da karuwar bukatar ma'adanai a duniya.

Taron wanda ya samu halartar jami’an gwamnati da ‘yan wasa masu harkar ma’adinai da masu zuba hannun jari na kasa da kasa, wani bangare ne na kamfen da gwamnatin Najeriya ke yi na bunkasa harkar ba hako ma’adinai kawai ba, har ma da sarrafa ma’adinan da aka hako a cikin gida.

A farkon shekarar nan ne gwamnatin Najeriyar ta ce za a bukaci sabbin masu zuba jari su kafa masana'antar sarrafa ma'adinai a cikin gida idan suna son samun lasisin hakar ma'adinai.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG