Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatan Hakar Mu'adinai Sun Yi Zanga Zanga a Rustenburg


Ma'aikata suna zanga zanga a bakin kamfanin Anglo American
Ma'aikata suna zanga zanga a bakin kamfanin Anglo American
Ma’aikatan hakar mu’adinai da dama a Afrika ta Kudu sun gudanar da zanga zanga yau asabar a Rustenburg domin nuna goyon bayansu ga dubban abokan aikinsu da kamfanin hakar karfen Platinum na Anglo American ya kora.

Kamfanin karfen platinum mafi girma a duniya ya kori ma’aikata dubu goma sha biyu a Rustenburg jiya jumma’a sabili da gudanar da yakin aikin da ya sabawa doka.

Kamfanin hakar karfen Platinum na Anglo American yace ma’aikatan kamfanin dake aiki a mahakar Rustenburg sun ki bayyana gaban kwamitin ladabtarwa dake zama dangane da yajin aikin.

Yayin zanga zangar da aka gunar yau asabar, magudun yajin aikin Gaddafi Mdoda ya yi gargadi da cewa, yana yiwuwa a fuskanci wani tashin hankali sakamakon matakin da kamfanin ya dauka.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG