Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Tace Zata Mayarwa Amurka Martani


Shugaban Kasar Amurka Donald Trump Da Shugaban Kasar Koriya Ta Arewa Kim Jon Un
Shugaban Kasar Amurka Donald Trump Da Shugaban Kasar Koriya Ta Arewa Kim Jon Un

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi sabuwar barazana akan gwajin makamin 'kare dangi da ake kyautata zaton 'kasar Koriya ta Arewa zatayi a 'karshen makon nan, inda yace “Za’ayi maganinsu”, abinda ya janyo martanin nan take daga wani babban jami’in gwamnatin ta Koriya a yau Juma’a.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Koriya ta Arewa Han Song Ryol yace “Idan Amurka tayi 'kokarin daukar wani mataki na ganganci to hakika zamu mai da martini da 'karfin dakarun Koriya ta Arewa”.

Han ya jaddada a wata tattaunawa ta musanman da yayi da kamfanin dillancin labarai na Associated Press, cewa “Muna da Makaman 'kare dangi masu 'karfi a hannunmu, ina tabbatar muku da baza mu nad'e hannuwanmu mu zuba ido akan Amurka ba”.

A jiya dai, Trump ya fad'i cewar Koriya ta Arewa na niyyar fasa wani makamin Nukiliya a 'kar'kashin 'kasa a gobe Asabar domin murnar kewayowar ranar kafa 'kasar da kuma wanda ya kafa ta wato Kim il sung.

Trump ya bayyana cewar “Koriya ta Arewa matsalace wacce za’a magance ta”.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG