Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamus Ta Ware Ranar 28 Ga Mayu Ranar Tsaftar Masu Jinin Al’ada, Wato "International Day For Menstrual Hygiene"


International Day For Menstrual Hygiene
International Day For Menstrual Hygiene

An ware ranar ce don karfafa muhimmanci kula da tsaftar jiki a lokacin da mace ke al’ada da kuma wayar da kan jama’a.

Wata kungiya mai zaman kanta a kasar Jamus da ake kira Wash United ce ta ware ranar 28 ga watan Mayu na kowace shekara a matsayin ranar tsaftar mata masu jinin al’ada, wato International Day For Menstrual Hygiene wadda ta samu karbuwa a duk fadin duniya.

An ware ranar ce don karfafa muhimmanci kula da tsaftar jiki a lokacin da mace ke al’ada da kuma wayar da kan jama’a game da irin matsalolin da matan da basa samun auduga (pad) a lokacin suke shiga.

Sa’an nan an kuma yi kira ga kungiyoyi masu zaman kansu, da masu ruwa da tsaki da ma sauran jama'a da su tattauna game da irin kalubalen da mata ke fuskanta a shekarun da suka isa yin al’ada.

Taken ranar na wannan shekarar shine ‘Jinin Al’ada ba abin kyama bane’.

Muryar Amurka ta zanta da Dr. Na’ima Idris kan wannan rana tare da jaddada muhimmancin tsafta a lokacin da mace ke jinin al’ada, tare da bada shawarwari don gujewa cututtuka sakamakon rashin tsafta.

Saurari cikkaken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

XS
SM
MD
LG