Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wasu Dalibai Da Malamai Bisa Zargin Satar Jarabawa


Duk da matakan tsaron da hulkumomin ilimi suka dauka akan jarabawa sai da wasu bata gari suka yi zatar jarabawa.

Yayinda ake gab da kammala jarabawar shiga sakandare a duk fadin kasar ta jamhuriyar Nijar, jami’an tsaro a garin Maradi sun damke wasu mutane da suka hada da dalibai da Malamai da ake zargin da satar jarabawa.

Mai kula da bada ilimi a yankin Maradi ta biyu Malam Dogo Rabe, ya tabbatarwa muryar Amurka afkuwar lamarin. Ya kuma kara da cewa mutane da dama suka shiga hannu akan wannan matsallar kuma hukumomin na ci gaba da gudanar da bincike.

Afkuwar wannan lamari na da daure kai ganin irin matakan tsaron da hukumar ilimi ta dauka na tabbatar da ganin cewa an tafiyarda takardun jarabawar cikin tsaro ta yadda za a kaucewa irin wannan amma gashi duk da matakan da gwamnati ta dauka hakkan ya faru.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:01 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG