Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wani Dan Najeriya Da Makamai A Jamhuriyar Nijar


A jamhuriyar Nijar 'yan sanda sun kama wani fasinja dan Najeriya, a mashigar birnin Yamai dauke da tarin bindigogi, da ya boye a cikin wata motar jigila.

Yana cikin wata motar jigilar da ta dauko shi daga garin Gao na arewacin Mali. Nasarar wannan kamun dai, dalilin karin mutunta tsarin binciken da kungiyar ECOWAS ta bullo da shi a baya domin tunkarar matsalar tsaro.

Kimanin bindigogi 19, wadanda suka hada da kirar sojoji 11, da pistol 7, da wata kirar china 1, aka gano a cikin wata motar jigila, kirar bus wacce ta fito daga garin Gao na arewacin Mali.

Jami’an tsaro a tashar bincike ta kauyen Bangoula dake gab da mashigar birnin Yamai ne suka gano wadanan makaman da aka cusa a buhuhuwan masara, mallakar Igiebor Samson Oraseti, wani dan Najeriya mai shekaru 60 a duniya.

A take aka wuce da shi zuwa ofishin ‘yan sandan unguwar Yantala dake gundumar Yamai ta 1, inda aka tsare shi.

Shugaban hadakar kungiyoyin direbobi da masu aikin sufuri, da shugaban kungiyar Syncotaxi Gamatche Mahamadou, sun ce faruwar irin wannan al’amari da rashin mutunta tsarin bincike ne, dalilin da kasashen yammacin Afirka suka bullo da shi bada dadewaba da nufin magance matsalar tsaro.

Motar dake dauke da wadanan makamai ta yi nasarar ratsa dukkan garuruwan dake kan hanyar da ta taso daga iyakar Mali, zuwa kewayen birnin Yamai, ratsawa ta jihar Tilabery.

Abinda ke haddasa mahawara a game da tasirin dokar ta bacin, da gwamnatin Nijar ta kafawa wannan yanki, bayan barkewar ayyukan kungiyoyin ta’addanci.

Tuni aka kaddamar da bincike akan wannan sabon al’amari mai nasaba da yanayin tabarbarewar tsaro, da ake da shi a arewacin Mali, yankin da ‘yan ta’adda, da ‘yan tawaye suka mamaye bayan bazuwar makaman da ake alakantawa da faduwar gwamnatin Gaddafi a Libya.

Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG