‘Yan sanda a Jamhuriyar Nijer sun gabatarwa manema labarai wasu gaggan ‘yan fashi da makamai, wadanda suka addabi jama’a a kewayen bankunan birnin Yamai, da wadanda ke kai farmaki a gidajen attajirai da ofisoshin kungiyoyi da kamfanoni masu zaman kansu.
Gungu na farko na ‘yan fashi na kunshe ne da mutane kimanin 15, wadanda suka hada da ‘yan kasashen Togo, Benin, Cote D’ivoire. Bayanai na nunin cikin kankanen lokaci suka yi nasarar kwace million kusan dari biyu (200) na CFA, a Yamai. Dubun wadanan barayi ta cika ne sakamakon hadin guiwar ‘yan sandan Gaya da takwarorinsu na Yamai. Nana Aichatou Bako ita ce mataimakiyar Darektan sashen watsa labarai a hukumar ‘yan sanda.
Sauran mutanen da suka fada komar ‘yan sanda sune wadanda ke bin dare suna kai sumame a gidajen attajirai da ofisoshin kungiyoyi masu zaman kansu, cikinsu har da wani mutunen da ya hallaka wata malamar makarantar da yake yiwa gadi a gidanta.
A yayinda ya ziyarci ofishin ‘yan sandan farin kaya don ganewa idanunsa wadanan ‘yan fashi alkali mai tuhuma da sunan hukuma wato, Procureur de la Republique Chaibou Samna, ya bayyana cewa dukkansu sun amince da laifuffukan da ake zarginsu da aikatawa, abin dake nufin za a gurfanar da su a gaban koliya don karbar hukunce-hukuncen da doka tayi tanadi.
A kalla million 329 na CFA da wasu ‘yan kai ne, aka bayyana cewa wadanan barayi sun yi nasarar kwata a hannun bayin Allah, tare da wasu na’urorin Komputa da dai sauransu.
Ga rahoton Wakilin muryar Amurka a yamai Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum