Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Babban Dan Jarida A Nijar Bayan Rufe Tasharsa


FILE PHOTO: Sahel junta leaders meet for a summit in Niamey
FILE PHOTO: Sahel junta leaders meet for a summit in Niamey

An kama Seyni Amadou, babban editan gidan talabijin na Canal 4, in ji kungiyar CAP-Medias-Niger, mai wakiltar ma'aikatan yada labarai a kasar. A ranar Juma'ar da ta gabata ma'aikatar sadarwa ta Nijar ta sanar da dakatar da tashar ta shi na tsawon wata guda.

Wata kungiya ta ce wani babban dan jarida a Jamhuriyar Nijar na tsare a jiya Assabar, kwana guda bayan da aka dakatar da tashar talabijin mai zaman kanta da yake gudanarwa, sakamakon wani rahoton sukar gwamnatin mulkin sojin kasar.

An kama Seyni Amadou, babban editan gidan talabijin na Canal 4, in ji kungiyar CAP-Medias-Niger, mai wakiltar ma'aikatan yada labarai a kasar.

A ranar Juma'ar da ta gabata ma'aikatar sadarwa ta Nijar ta sanar da dakatar da tashar ta shi na tsawon wata guda.

Tashar talabijin ta kasar, Tele Sahel ta ce an dauki matakin kan Canal 3 TV "saboda karya ka'idojin aikin."

Tashar ta Canal 3 ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na faransa na AFP a cikin wata sanarwa cewa, dakatarwar na da nasaba da watsa shirye-shiryen da aka yi kan matsayin ministoci a gwamnatin Fira Minista Ali Mahaman Lamine Zeine, wani farar hula da gwamnatin sojan ta nada.

A cikin kididdigar rahoton, an dora Zeine a matsayin na farko, yayin da kuma aka lissafa da yawa daga cikin ministocinsa a zaman marasa karfi a gwamnatin.

A cikin wata sanarwa da CAP ta fitar ranar Juma’a, ta yi Allah wadai da kama Amadou da tsare shi, tare da yin kira da a mutunta ‘yancin ‘yan jarida.

Ta kara da cewa, "Ba'a taba yin watsi da matakin dakatar da kafafen yada labarai a Nijar a tarihin hukumar zartarwa ba, ciki har da wasu lokuta na musamman."

CAP ta yi kira ga Ministan Sadarwa Sidi Raliou Mohamed da ya sake duba matakin nasa.

Janar Abdourahamane Tiani, babban hafsan hafsoshin tsaron fadar shugaban kasar Jamhuriyar Nijar, a shekara ta 2023 ya hambarar da shugaba Mohamed Bazoum, babban aminin kasashen yammacin duniya wajen yaki da jihadi a yankin kudu da hamadar Sahara.

Tun bayan juyin mulkin ne dai mahukuntan mulkin sojan Nijar suka juya wa Faransa da ta yi musu mulkin mallaka baya, tare da kulla alaka da wasu 'yan mulkin sojan Burkina Faso da Mali da kuma Rasha.

Haka kuma ta rufe wasu tashoshi na kasa-da-kasa da suka hada da Radio France International (RFI), France 24 da BBC.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG