Tsohon shugaban zauren Majalisar Dinkin Duniya John Ashe da ake zarginsa da hannu a cin hanci da rashawa a Majalisar Dinkin Duniya ya samu beli kuma an sakoshi daga kurkuku dake birnin New York.
Masu shigar da kara sun ce tana yiwuwa Mr. Ashe ya kara fuskantar wasu tuhume tuhumen. An saki Mr. Ashe din ne akan kudin beli na dalar Amurka miliyan daya.
Tun can farko ana tuhumar Mr. John Ashe da laifuka biyu da suka jibanci kin biyan haraji. To saidai har yanzu masu gabatar da kara basu tuhumeshi da zargin cin hanci ba saboda kariyar diflomasiya da watakila yana da ita.
Masu gabatar da kara suna zargin Mr Ashe tsohon jakadan Majalisar Dinkin Duniya a kasashen Antigua da Barbuda da karban dalar Amurka fiye da miliyan daya a matsayin na goro daga wani dan kasar Sin saboda ya taimaka ya tallata kamfanin mutumin. Sun kuma zargeshi da kin biyan haraji akan kudaden cin hanci da ya tara.
Banda Mr. Ashe mahukunta na kuma zargin wani hamshakin attajiri da ya mallaki biliyoyin dala kuma mazaunin kasar Makau mai sana'ar gine gine Mr. Ng Lap Seng. An kuma sanshi da suna David Ng tare da wasu sunaye uku.
Shi Mr. Ng an cafkeshi watan jiya dangane da wasu tuhume tuhume daban daga bisani aka yi masa daurin talala da sa dala miliyan 50 a matsayin kudin beli.