•Ikon kamawa ko tsare mutanen da ake zargi
•Kamewa da kwace duk wani gini ko fili ko wani abu da ake amfani da shi wajen shiryawa ko aikata ayyukan ta’addanci
•Killacewa da hana shiga ko fita daga duk wani yankin da za a gudanar da aikin farautar ‘yan ta’adda
•Gudanar da bincike
•Kama mutanen da suke dauke da makamai ba tare da iznin hukuma ba
•Neman jama’a da su hada kai da hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa an kammala aikin tsaro cikin kankanin lokaci
•Kiamar yadda aka yi a baya, za a bukaci kasashe makwabta da su bayarda hadin kai wajen kama duk wasu ‘yan ta’addar da zasu tsallake bakin iyaka su shiga cikin wata kasar
• Gwamnoni da sauran wadanda ke rike da mukaman siyasa na wadannan jihohi zasu ci gaba da rike kujerunsu da gudanar da ayyukansu kamar yadda tsarin mulki yace.