An kaddamar da wannan shirin ne a filin saukar jiragen sama a birnin Maiduguri. An kuma gwada yanda za a rika saukar da abinci a sansanonin ‘yan gudun hijira a wuraren dake gama da matsalar tsaro a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
An yi bukin kaddamar da shirin a gaban ministan ma’aikatar agaji da jinkai ta kasar, inda aka sauke wasu daurin abinci daga jirgi mai saukar ungulu ta sama ta hanyar kumbo da aka kira “Parachute” a turance, da kuma aka ce haka za a rika aiwatarwa a irin wuraren da ake fama da matsalar tsaro.
Ministar ma'aikatar Hajia Sadiya Umar Faruk ta ce “mun zo ne domin mu duba kuma mu binciki wuraren da motoci basu iya kaiwa saboda da wadansu dalilai, mu kuma ga hanyar da zamu yi aiki tare da ma’aikatar sojin Najeriya musamman rundunar sama, kana mu tabbatar idan ba za a iya bi ta kasa a kai abinci ba, akwai wata hanya da za a kai abinci ga ‘yan gudun hijira”.
Ministar ta ce zasu yi iya kokarin su domin su tabbatar da abinci ya shiga hannun wadanda ake niyar basu, a don haka sai an bincika an ga wurare ne da masu bukata suke ko kuma wuri ne da ‘yan ta’adda suke.
Kwamandan jami’in sojan, Pateince Amade ya yiwa manema labarai karin haske a kan yadda zasu gudanar da aikin su. “Ya ce sajojin saman Najeriya suna da karfin samar da abinci ta sama ga mabukata ta hanyar jirgi mai saukar ungulu.
Mataimakin gwamnan jihar Borno Alhaji Umar Usman Kanaburu ya bayyanawa ministan irin asarar da gwamnatin jihar ta yi sakamakon hare haren na ‘yan kungiyar Boko Haram.
Daga Maiduguri ga dai rahoton Haruna Dauda Biu:
Facebook Forum