Jiya 15 ga watan Oktoba aka yi bukin ranar matan karkara ta Duniya, da nufin tunatar da gwamnatocin kasashe masu tasowa irin nauyin da ya rataya a wuyansu, a game da halin da mata ke ciki a yankunan karkara ta yadda za a dauki matakan magance wahalhalun da suke fama da su.
Rahotannin bincike na Majalisar Dinkin Duniya na nuni da cewar mace 1 daga cikin 3 a duniya na rayuwa ne ta hanyar ayyukan noma, kiwo, saboda haka a bana aka daukaka shagulgulan ranar ta matan karkara. Don neman hanyoyin karfafa matakan inganta rayuwar mata da ‘yan matan karkara, ganin yadda illolin canjin yanayi ke haifar da cikas ga harkokinsu.
Hajiya Halima Sarmaye, wata mai fafutukar kare hakkin mata ta bayyana gamsuwa da wannan yunkuri da ta ce ya yi dai-dai da yanayin da matan yankin Sahel ke ciki a yau.
Haka kuma binciken na MDD ya gano cewa kashi 80 daga cikin 100 na gidajen da ke da matsalar ruwan sha a karkara, na dogaro ne da mata da ‘yan mata wajen nemo ruwan da zasu yi amfani da su.
Wannan na daga cikin matsalolin da a yau aka gano cewa suna yiwa ilimin mata tarnaki a kasashe masu tasowa, yayin da abin ke shafar lafiyar mata a karkara.
Ga cikakken rahoto daga wakilin muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum