Rayuwa da ilimi jami’a ya sha baban baban da yadda ake gudanar da rauyawa wajen neman ilimi a sauran makarantu kamar yadda Salma Muhammad ta bayanawa wakiliyar Dandalinvoa Baraka Bashir.
Tace ta fuskanci ‘yar targanda a lokacin da na tsinci kanta a jami’a kasancewar da kamala karatuna na sakandare kawai sai ta sami damar shiga jami’a ba tare da ta sami wani bita na yadda zata fuskanci karatu a jami’a ba.
Malama Salma ta ce ta samu damar karantar aikin jarida amma ba abinda ta so karantawa ba Kenan , tace taso ta karanci harkar banki dangogin lissafi da tsimi da tanadi.
Ta kara da cewa ta fuskanci kalubale da dama domin harshen turanci na daga cikin kwasaikwasan da ke bata wahala sai ga shi ta tsinci kanta a fannin harshe da ke bukatar turanci.
Ta ce a lokacin da take matakin karatu na uku sai ta sami damar koyon aiki a wani gidan Radiyo inda a nan ne ta fuskanci alkibliar yadda aikin jarida yake kuma a sannan ne ta ji sha’awar aikin jarida.
Salma ta shawarci ‘yan uwanta matasa da su dage wajen neman ilimi duba da irin tarin alfannun da ilimin Boko ke da shi ga rayuwar diya mace ko da kuwa bata aiki.
Facebook Forum