Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gwabza Kazamin Fada A Baga, An Kashe Mutane Da Yawa


Hoton da aka dauka da wayar salula ta wata yarinya tsaye a kangon gidaje a garin Baga, lahadi 21 Afrilu, 2013.
Hoton da aka dauka da wayar salula ta wata yarinya tsaye a kangon gidaje a garin Baga, lahadi 21 Afrilu, 2013.

Wani jami'i a yankin yace an kashe mutane har 185, cikinsu har da sojoji da fararen hula da kuma 'yan kungiyar nan ta Boko Haram.

An kashe mutane dama a yankin arewacin Najeriya a lokacin wani kazamin fadan da aka gwabza a tsakanin dakarun tsaron gwamnati da wasu ‘yan kishin Islama.

Wani jami’i mai suna Lawan Kole yace mutane 185 suka mutu, koda yake kamfanin dillancin labarai na Faransa ya ambaci wani kakakin rundunar sojoji a Jihar Borno yana mai fadin cewa an yi karin gishiri a wannan adadin da aka bayar.

An fara gwabza wannan fada ranar jumma’a da maraice a garin Baga dake bakin tabkin Chadi, abinda ya sa dubban mutane suka gudu daga wannan garin da ya shahara wajen kamun kifi.

Mutanen garin na Baga sun ce an goce da fada a lokacin da sojoji suka kewaye wani masallacin da aka yi zargin cewa ‘yan kungiyar nan ta Boko Haram sun buya a ciki.

An yi musanyar wuta sosai, inda aka ce ‘yan kungiyar ta Boko Haram sun yi amfani da muggan makamai ciki har da gurnetin da ake cillawa da roka. Sojoji da kuma jami’an yankin sun ce ‘yan kungiyar sun yi amfani da fararen hula a matsayin garkuwa, yayin da mazauna garin suka ce da gangan sojoji suka yi ta cinna wuta a gine-gine lokacin wannan harin.

Mutanen da suka mutu sun hada da fararen hula, da sojoji da kuma ‘yan kungiyar Boko Haram, amma ba a samu tabbacin ainihin yawan wadanda suka mutun ba.

An shafe sa’o’i da dama ana gwabza wannan fada a daren jumma’ar, amma labari bai iso Abuja babban birnin Najeriya ba sai jiya lahadi.

Hukumomin Najeriya su na dora ma kungiyar Boko Haram laifin munanan hare-haren bam da harbe-harbe a arewacin Najeriya kama daga shekarar 2009. Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch ta ce tashin hankali mai nasaba da kungiyar Boko Haram yayi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 3, adadin da ya hada har da mutanen da jami’an tsaron Najeriya suka kashe.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG