Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Taron Zaman Lafiya Da Tsaro Na Kofi Annan A Ghana


Shugaban Kasar Ghana Da Wasu Da SUka Haarci Taron Zaman Lafiya Da Tsaro Na Kofi Annan (KAPS Forum)
Shugaban Kasar Ghana Da Wasu Da SUka Haarci Taron Zaman Lafiya Da Tsaro Na Kofi Annan (KAPS Forum)

Taron, wanda yake karo na uku, ya gudana akan batutuwan hijira, tashe-tashen hankula, da juriyar al'umma a Afirka.

ACCRA, GHANA - Taron na kwanaki biyu da aka shirya a cibiyar horar da zaman lafiya ta kasa da kasa ta Kofi Annan (KAIPTC) da ke birnin Accra, ya hada tsofaffin shugabanni, shugabannin hukumomi da jami’u da kuma manyan masana domin yin nazari kan musabbabin yin hijira da tasirinta ga tsaro da zaman lafiyar al'umma a Afirka.

Taron Zaman Lafiya Da Tsaro Na Kofi Annan (KAPS Forum) A Ghana
Taron Zaman Lafiya Da Tsaro Na Kofi Annan (KAPS Forum) A Ghana

Da yake jawabi a wurin taron, mai taken, "Hijira da juriyar al'umma a tsarin duniya daban-daban: Magance rikice-rikice da gina zaman lafiya a Afirka", Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, ya jaddada cewa hijira na daya daga cikin batutuwan da suka fi daukar hankali da muhimmanci a duniya kuma ko shakka babu za ta kasance a tsakiyar ajandar ci gaban duniya da tsaro cikin gomman shekaru masu zuwa.

Shugaban Kasar Ghana Ya Na Jawabi A Lokacin Taron Zaman Lafiya Da Tsaro Na Kofi Annan (KAPS Forum)
Shugaban Kasar Ghana Ya Na Jawabi A Lokacin Taron Zaman Lafiya Da Tsaro Na Kofi Annan (KAPS Forum)

Dangane da halin da kungiyar ECOWAS ke ciki a halin yanzu na fama da matsalolin rashin tsaro da suka hada da tsatsauran ra'ayi da kuma juyin mulkin demokradiyya, shugaban yace: “Tare da takwarorina na ECOWAS muna neman bakin zaren magance kalubalen hade kan ECOWAS. Yankin yana cikin tsaka mai wuya kuma matakan da za mu dauka su ne za su tabbatar da yanayin da zai tsara hanyar ci gaba ko kuma halakar al’ummarmu"

Lokacin Taron Zaman Lafiya Da Tsaro Na Kofi Annan (KAPS Forum) A Ghana
Lokacin Taron Zaman Lafiya Da Tsaro Na Kofi Annan (KAPS Forum) A Ghana

Shugaba Akufo-Addo ya yi kira ga mahalarta taron da su yi la'akari da muhimman tambayoyi game da nau'in hadin kan duniya da zai inganta moriyar juna na yin hijira tsakanin kasashen da aka bari da kuma inda aka nufa.

Babban Darektan Cibiyar Al'adun Dimokradiyya da Yanci na Kasa da Kasa (CDHRI), Yunus Swalahudeen Wakpenjo, a tsokacin da yi kan taron, ya bayyana muhimmancin taron ga tsaron kasa da kasa kuma ya kara da cewa: “Duk shugabanni da suka yi jawabi a taron, sun yi magana ne da ya shafi ci gaba da kwanciyar hankali da zaman lafiya a duniya baki daya”.

Taron Zaman Lafiya Da Tsaro Na Kofi Annan (KAPS Forum) A Ghana
Taron Zaman Lafiya Da Tsaro Na Kofi Annan (KAPS Forum) A Ghana

Wasu tsoffin shugabanni, wakilai daga Majalisar Dinkin Duniya, da Tarayyar Afirka, da na ECOWAS, da Tarayyar Turai da shugabannin shige da fice daga kasashe daban-daban, da masana sun ba da ta su gudunmawar, a maudu’ai da suka hada da; hijira, sauyin yanayi da rikice-rikice a Afirka; magance hijira ba bisa ƙa'ida ba da sauransu.

Manazarci kan al’amuran yau da kullum, Issah Mairago Gibril Abbas ya yi wa Muryar Amurka bayanin jawabin da ya ja hankalinsa a taron shi ne, “jawabin shugaban Ghana, Nana Addo Akufo-Addo, wanda ya yi kan muhimmancin kaura a tsakanin kasashen yammacin Afirka da kuma barazana na tsaro da wannan kaura yake janyowa wadannan kasashen da yankin Sahel, lura da cewa ‘yan ta’adda suna safarar makamai da miyagun kwayoyi tsakanin wadannan kasashen”.

Lokacin Taron Zaman Lafiya Da Tsaro Na Kofi Annan (KAPS Forum) A Ghana
Lokacin Taron Zaman Lafiya Da Tsaro Na Kofi Annan (KAPS Forum) A Ghana

Taron ya samu halartar tsohon shugaban kasar Benin Boni Yayi, tsohon Firai Ministan Habasha Hailemariam Dessalegn Boshe, tsohuwar mataimakiyar shugabar kasar Gambia Uwargida Fatoumata Jallow Tambajang, tsohon mataimakin shugaban kasar Laberiya, Cif Dokta Jewel Howard-Taylor, da kuma babban wakilin kungiyar Tarayyar Afirka kan hana harbe-harbe, Dr. Mohamed Ibn Chambas.

Saurari cikakken rahoto daga Idris Abdullah:

An Gudanar Da Taron Zaman Lafiya Da Tsaro Na Kofi Annan (KAPS Forum) A Ghana.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG