Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rugujewar Gada: Babu Shaidar Dake Danganta Harin Da Ta’addanci – Gwamnan Jihar Maryland


Daga hannun hagu: Gwamnan jihar Maryland, Wes Moore.
Daga hannun hagu: Gwamnan jihar Maryland, Wes Moore.

Gwamnan Jihar Maryland, Wes Moore, ya kore yiyuwar harin ta'addanci sakamakon rugujewar wata muhimmiyar gada a birnin Baltimore da safiyar yau talata bayan da wani jirgin ruwan dakon ya afka mata.

WASHINGTON DC - A cewar Wes Moore binciken farko ya nuna cewar hadari ne ya afku kuma babu wata shaidar dake danganta hakan da harin ta'addanci."

Ya kuma sha alwashin samarda dukkanin abinda ake bukata domin aikin ceto sa'annan ya bayyana godiya ga jami'an bada agajin da suka fara kawo dauki saboda jajircewar da suka nuna.

"Har yanzu muna kan bincike game da abinda ya faru, saidai muna tattara bayanai cikin gaggawa. binciken farko ya nuna cewar hatsari ne ya afku. Bamu samu cikakkiyar shaidar dake danganta abun da harin ta'addanci ba".

Ababen hawa da dama sun afka cikin ruwan kogi mai sanyin gaske da sanyin safiyar yau Talata, jami'an bada agaji na kokarin lalubo wadanda keda sauran numfashi.

Moore ya kara da cewar, matukan wani jirgin ruwan dakon kaya sun hadu da ibtila'in daukewar lantarki sa'annan sun aike da sakon neman agajin gaggawa 'yan mintuna gabanin jirgin ya afkawa gadar "Francis Key Scot", al'amarin da ya baiwa hukumomi takaita zirga-zirgar ababen hawa a yankin da al'amarin ya faru.

An samu nasarar ceto mutane 2 daga cikin kogin, saidai ba'a tantance yawan mutanen da suka saura a cikin ruwa ba.

''Mumunan Hatsari''

Biden
Biden

Da yake jawabi kan rugujewar gadar, Shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya ayyana lamarin a matsayin mumunar hatsari inda ya yi alkawarin sake gina babbar tashar jiragen ruwa dake gabashin kasar nan take.

Shugaban ya kuma ce za a sake gina gadar ta Francis Scott Key nan take duk da cewa zai dauki tsawon lokaci.

Ya kara da cewa ce zai tabattar masu gudanar da aikin sake gina gadar sun sami duk kayayyaki da suke bukata daga gwamnatin tarayya saboda ganin sun sake gina gadar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG