Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Samun Kwanciyar Hankali A Paris


Masu zanga-zanga a Paris
Masu zanga-zanga a Paris

Ministan harkokin cikin gida a Faransa Christopher Castaner yace an samu kwanciyar hankali a rikicin jiya Asabar a birnin Paris duk da hargisti da aka samu nan da can, lamarin da yace bai dace ba.

“Yan sandan Faransa da taimakon rokoki sun zubawa masu zanga-zangar dake saye da riguna launin ruwan dorawa barkonon tsohuwa a kan titin Champs Elysees. Masu zanga-zangar suna kalubalantar tsadar rayuwa ne da ake fama da shi a Faransa.

Castaner ya kiyasta masu zanga-zangar da yawansu ya kai dubu goma a kan titunan Parisians suna cikin mutane dubu dari da dubu ashirin da biyar da suke zanga-zanga a fadin kasar.

Yace an kama kusan mutane dubu daya a birnin Paris kana mutane dari da talatin da biyar sun jikata ciki har da jami’an ‘yan sanda goma sha bakwai.

An jibge ‘yan sanda dubu tamanin da takwas a fadin kasar baki daya, a matsayin kari a kan ‘yan sanda dubu sittin da biyar da aka jibge a karshen mako yayin da zanga-zangar kin jinin tsadar rayuwar da ya barke, lamarin da ya kai ga raunata mutane dari da talatin da biyar.

Shugaba Emmanuel Macron ya kai ziyarar bazata da yammacin shekaranjiya Juma’a ga jami’an tsaron a wajen birnin Paris kuma ya yi musu godiya da aiki da suek yi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG