Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Yarinya 'Yar Kasar Kamaru Ta Sami Lambar Yabon Zaman Lafiya


 Divina Maloum
Divina Maloum

Wata yarinya ‘yar shekaru goma sha biyar daga kasar Kamaru tana daya daga cikin yara biyu da suka lashe lambar yabon wanzar da zaman lafiya ta kasa da kasa ta shekara ta dubu biyu da goma sha tara .

An ba Divina Maloum wannan lambar yabon ne sabili da kokarinta na yayata batun ‘yancin kananan yara da kuma gargadinsu kada su shiga kungiyoyin dake daukar makamai kamar Kungiyar Boko Haram

Daruruwan yaran makarantu a Yaounde, sun kafa ido a akwatunan talabijin ranar Laraba suna tafawa lokacin da aka ba Divina Maloum lambar yabon wanzar da zaman lafiya ta kananan yara, ta shekara ta dubu biyu da goma sha tara, a birnin Hague. A daidai lokacin da ake bukin ranar kananan yara ta duniya.

Maloum ta kafa wata kungiya da ake kira Kananan yara masu hankokoron zaman lafiya da ake kira "Children for Peace" “ da turanci, a shekara ta dubu biyu da goma sha hudu bayanda ta ziyarci arewacin kasar inda Kamaru ke iyaka da Najeriya, wurin da kungiyar Boko Haram ta kashe sama da mutane dubu ishirin da bakwai ta kuma raba sama ta miliyan biyu da matsugunansu.

Yanzu kungiyar "Children For Peace" tana da membobi kananan yara dari a yankuna goma na kasar Kamaru, Kungiyar ta kuma shirya taruka tsakanin al’umma da kuma kafa kulob kulob na wanzar da zaman lafiya a masallatai, wadanda suka hada kai da sauran yara, suka kuduri aniyar nisanta kansu da tsats-tsauran ra’ayi.

Maloum tace ta hakikanta cewa, kowa yana iya taka rawa a sami zaman lafiya tsakanin al’umma.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG