Ranar daya ga watan Janairun wannan shekarar da misalin karfe biyu Hidaya ta fita ta kai gyaran rigunanta a wani shago mai kallon gidansu. Da ta je shagon sai ta ganshi a rufe to sai ta yi gaba domin ta sayi katin waya na nera dari biyu. Tana kan hanya sai wasu mutane biyu suka tambayeta layin Kabiru Gaya. Iyakacin abun da ta iya tunawa ke nan.
Bayan da iyayenta basu gani ta dawo ba yadda ta saba idan ta fita sai suka shiga cigiya. Da yake ranar daya ga wata ne sai suka bi duk inda suka ji an yi fati ko wasannin sabuwar shekara da zaton ko ta je wurin. Duk neman da suka yi basu sameta ba basu kuma ci karo da wani wanda ya ce ya ganta ko inda ta nufa ba. Lamarin ya kada iyayenta da 'yanuwa.
Wadanda suka sace ta sun fita da ita ne daga Kano.Ko da ta farfado ta samu kanta a wani gida cikin birnin Fatakwal fadar gwamnatin jihar Rivers. Sun hada ta da wasu yaran da suka hada da maza da mata. Ta ce kullum da safe suna raba masu ayyukan da zasu yi kamar shara da wanke-wanke. Daga bisani suka sa wani karfe cikin wuta suna danna masu a jiki domin su basu lambar shaida.
Hidaya ta cigaba da zama a gidan da sauran yaran har wasu suka dauketa ita kadai suka kaita jihar Imo. Daga nan ne suka sata cikin wata motar zuwa Kano. Ta dawo wurin iayayenta ba tare da an yi mata wani abu ba. Hidaya dai yar shekara 15 ce da haihuwa.
Ga karin bayani.