Yara mata kimanin su 37 da akayi fataucinsu zuwa kasar Mali, wadanda yanzu haka aka mayar da su Najeriya, inda suke hannun hukumar yaki da safara da kuma bautar da mutane ta Najeriya (NAPTIP), yayin da ake saisaita musu tunani kuma ake tatsar bayanai daga garesu.
Hukumar NAPTIP tace ‘yan sandan kasar Mali ne suka kama yaran suna yawo akan tituna domin yin karuwanci, hakan yasa hukumar tare da hadin gwiwar ma’aikatan tsaron Najeriya suka sa hannu wajen dawo da su Najeriya.
Haka kuma hukumar ta ce zata ci gaba da aiki don ganin an dawo da sauran ire-iren ‘yan matan da aka kai sauran kasashe domin aikata karuwanci.
Dakta Husaini Abdu babban jami’in cibiyar Plan International dake sa ido kan harkar yara, yace matsanancin talauci da kuma son kai sune aba’isin sanadiyar fataucin kananan yara.
Wannan dai ba shine karo na farko da wannan hukuma ke dawo da yara mata daga kasar Mali ba, domin ko a shekara ta 2012 hukumar ta dawo da wasu yara mata har 104.
Domin karin bayani ga rahotan Hassan Maina Kaina daga Abuja.
Facebook Forum