WASHINGTON, DC —
An Cafke wani mutun a kasar Afirka ta kudu, bayan da aka sameshi da wasu sassan jikin mata, kimanin guda ashirin da daya a cikin gidan kankara ajiye a gidansa.
Hukumar 'yan Sanda ta Afirka ta Kudun ta ce an samu magunguna da ake amfani dasu a wajan tiyata a gidan sa, mutumin mai shekaru 58, yana kuma da aure da 'ya 'yansa biyu.
Kakakin 'yan Sandan Hangwani Mulaudzi, ya ce ba'a tabbatar da ko mutane nawa ne wannan aika aika ya shafa ba yana mai cewa hukumar ta samu labarin ne ta bakin daya daga cikin wadanda aka yiwa wannan tu'annatin.
Ya kara da cewa masanan kimiyar jikin bil-Adama, na ci gaba da binciken tantance bangarorin da aka gano kuma za'a gufanar da wanda ake zargi a gaban kotun a yau litini din nan.