Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fara Tunaninn Aure Tsakanin Samari Da 'Yan Mata


Akwai dalilai da dama da ka iya sa saurayi da budurwa su amince da kuma yardarm ma juna domin a daura masu aure. Mafi muhimmanci shine gano wadannan dalilai, dan haka a naka ra’ayin wadanne dalilai ne za su sa kaji cewar lokacin ka na yin aure ya yi?

Tsawoncin lokacin da ka dauka kana soyayya ne?

Ko kuwa sai ka jira magabatan ka sun yanke hukuncin hakan?

Wadanne alamu zaka lura da su da za su sa kaji cewar wadda kake nema lallai ta cancanci ka aure ta?

Idan ka yanke wannan shawarar, ta yaya zaka gabatar wa da budurwar ka ko saurayin ki cewar ya kamata kuyi aure? Me zaku ce?

Yanke shawarar yin aure ga matasa na tattare da kalubale da dama musamman a wannan zamanin, amma yana da matukar amfani idan ma’aurata za su zauna su amince da juna sa’annan su tsayar da duk shawarar da suka ga ta yi daidai da su.

Akwai kuma bukatar fayyace ma juna gaskiya da kokarin hangen gaba da kuma tsara yadda suke so rayuwar su ta kasance. Wani lokaci ma har suna iya yarda da juna domin tsara iyalin da suke so su samu da ilimin da suke so suba iaylin na su.

Aura zai iya kasancewa mai matukar dadin gaske musamman idan saurayi da budurwa suka kalli kansu a matsayin wadanda suke niyyar zamam tare har matuka, da mutunta juna da da kuma zama abokai na kud da kud wadanda suka yarda da juna kuma za su iya tsaya ma juna a kowane hali.

Saurari Karin Bayani.

XS
SM
MD
LG