Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daga Cin Abincin Turawa "Bear" Ya Sheka Bacci


Dabba Bear
Dabba Bear

A jihar Colorado ta kasar Amurka, wani dabba da ake kira “Bear” a turance, ya bayyana a kusa da wata makaranta. Hakan yasa an kulle makarantar, kuma hukumomi sun shiga binciken ko ina dabbar ya shige, ganin dabbar a cikin gari na nuna alamun yunwa ta koro shi daga daji.

Ashe bear din, ya shiga wani shagon masu saida abincin turawa da ake kira “Pizza” ya kuma samu wani sinadari da ake hada ita pizzar, mai suna “Icing” ya ci mai isar shi, daga nan kuwa sai yakama bacci a cikin shagon. Daya daga cikin ma’aikatan wannan shagon ya shiga cikin shagon don gudanar da aiki, sai ya ga dabbar na ta shararar bacci.

Hukumomi sun samu damar kama dabbar don maida shi cikin daji. Su dai wadannan dabbobin su kan yi rayuwar cikin daji, suna gudun mutane, amma idan kuma aka kure su, su kan yima mutun lahani, domin kuwa suna da kunbuna kamar sauran namun daji. Mafi akasarin jihohin kasar Amurka, suna da wadannan dabbobin da dama.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG