Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sanata Bukola Saraki Zai Koma Kotu


Sanata Bukola Saraki
Sanata Bukola Saraki

Bisa dukan alamu nasarar da Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki ya samu a Kotun da'ar ma'aikata ta yi doro domin Ministan Shari'a Abubakar Malami ya daukaka Kara a madadin Gwamnatin Tarayya.

Daukaka kara ta Abubakar Malami, ta biyo bayan wanke Sanata Bukola Saraki da kotu tayi da soso da sabulu, da gwamnatin tarayya ta nuna cewa akwai sauran rina a kaba.

Ministan Shara’a Abubakar Malami, a wata takarda ta masamman ya nuna cewa wannan yaki na cin hanci da rashawa abune da gwamnatin tarayya zata tabatar da aiwatar dashi domin tsaftace sha’anin shugabanci da aiyukan yau da kullum tsakanin al’umar Najeriya.

A cewar minstan kara bata kammaluwa sai an kure daukakata har zuwa kotun koli domin zartar da hukunci a inda yace wanna ma sai an bi sau da kafa domin gano gaskiya al’amarin da ya jibanci tuhumar da ake yiwa Bukola Saraki.

Hukunci da kotu ta zartar da ya wanke Sanata Bukola Saraki, yasa ra’ayoyi sun banbanta a tsakanin ‘yan majalisa masamman ma dashi Ministan Shara’a Malami, ya sha alwashin daukaka kara akan wannan al’amarin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:25 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG