A wata rubutaciyar takardar jawabi da Jamiyar Hope Democratic Party ta raba wa manema labarai na nuni da cewa sun shigar da karar ne a bisa wasu dalilai da dama, amma muhinmi dalili shi ne cewa akwai wata shari'a da aka riga aka shigar dake kalubalantar nasarar da shugaba Mohammadu Buhari ya samu a zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu na wanan shekara.
Wani kwararre a bitar kundin tsarin mulki Barista Mainasara Kogo Ibrahim ya yi fashin baki a kan ko Jamiyar Hope Democratic Party tana da hurumin shigar da irin wannan kara bayan an kammala shirye-shiryen rantsar da shugaban kasar. Barrister Mainasara ya ce zata iya shigar da kara amma kuma matakin zai haifar da rudani.
A nashi jawabi, tsohon shugaban hukumar wayar da kan al'umma ta Kasa Dokta Mike Omeri ya ce duka da cewa Jamiyar Jamiyar Hope Democratic Party tana da hurumin shigar da kara amma a yi taka tsantsan saboda duk abin da kotu zata yi, a bi abin da dokar kasa ta tanada domin kada a jefa kasa a cikin wani halin kakanakayi.
Jamiyar Jamiyar Hope Democratic Party ta ce an riga an kaiwa shugaba Buhari takardar karan dake bayanin cewa in har an dasa ayar tambaya a wajen Kalubalantar zaben nasa, toh bai cancanci daukar rantsuwa ba.
Sai dai a daidai lokacin daukan wanan rahoto fadar shugaban kasa ba ta mayar da martani ba.
Medina Dauda daga Abuja Najeriya nada karin bayani:
Facebook Forum