Matakin da ofishin jakadancin Amurka ya dauka na dakatar da sabunta VISA ta hanyar tura sako ga wadanda su ka taba zuwa kasar, ya sa matafiya da mu ka zanta da su danganta hakan da yanayin tsaro.
Ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ya fitar da sanarwa ta matakin, da cewa daga yanzu ofishin ba zai ci gaba da sabunta VISA ta tsarin “DROPBOX” wato sakon bukata ta na’ura mai kwakwalwa ko aika bukatar ta hannun kamfanonin kai sako na DHL daga wadanda su ka taba samun VISA don a sabunta mu su ba.
Yanzu dai ya zama wajibi mai bukagtar sabunta VISA ya rubuta bukatar a yanar gizo daga nan ya bayyana ofishin jakadancin don yi ma sa tambayoyi; wanda a baya an dauke wa wadanda su ka taba samun VISA wannan dawainiyar.
Dr.George Uboh ya ce ya fara zuwa Amurka tun 1984 kuma a can din ma ya yi karatu, ya nuna ba laifi Amurka ta dau wannan mataki don matakan tsaro.
Uboh ya ce dama lamarin ba da VISA hakki ne na kasa da ta ke da iko ta ba wa wanda ta ga dama ko ta hana, kuma ko da ma mutum ya samu VISA bai zama lalle ya samu shiga kasar da ta ba shi damar ba.
Shi ma wani Injiniya Magaji Muhammad Yaya na da ra’ayin Amurka ba ta sako-sako da lamarin tsaro kuma ba mamaki akwai abun da ta hango ne ya sa ta dau sabon matakin.
A tsarin ofishin jakadancin Amurka, ya kan fitar da sanarwa kuma shikenan iya bayanin kenan ba wani sabon karin haske da za a iya samu.
Ga sauran bayanin rahotun daga: Saleh Shehu Ashaka.
Facebook Forum