‘Yan Najeriya sun bazama a shafukan sada zumunta, suna taya Leah Sharibu murnar cika shekaru 16, yayin da mayakan kungiyar Boko Haram ke ci gaba da garkuwa da ita.
Daga cikin ‘yan Najeriyan, har da sanatoci da suka hada da Sanata Ali Ndume mai wakiltar kudancin jihar Borno da Sanata Ben Murray Bruce da ke wakiltar gabashin jihar Bayelsa, da wani lauya mai fafutuka da ake kira Reno Omokri.
Sanatocin sun bayyana ne a wani hoton bidiyo da Omokri ya wallafa a shafinsa na Twitter, sanatocin suka taya matashiyar murnar zagayowar ranar haihuwarta.
“Muna fatan alherin da ke cikin watan Ramadana ya taba zukatun wadanda ke rike da ke, su sako ki.” Inji Ndume, wacce jiharsa ke makwabtaka da ta Leah.
A ranar 19 ga watan Fabrairun bara, mayakan na Boko Haram suka sace ‘yan mata 110 a makarantar Sakandare ta Dapchi a karamar hukumar Yunusari da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya.
A ranar 21 ga watan Maris hukumomin Najeriya suka bayyana cewa an sako matan, bayan wata matsaya da aka cimma da mayakan.
Amma daga cikin daliban da aka sako, babu a wata daliba mai suna Leah Sharibu.
Shaidu daga cikin daliban da aka sako, sun ce an ki sakin Sharibu ne saboda ta ki amincewa ta zama musulma bayan da mayakan na Boko Haram suka nemi ta karbi addinin.
Wannan lamari ya ja hankulan duniya baki daya, inda kungiyoyin masu fafutuka da masu kare hakkin bil Adama da masu fada a ji, suka yi ta sukan hukumomin Najeriya saboda sun gaza karbo Leah.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana iya bakin kokarinta wajen ganin an saki matashiyar.
Sai dai wasu na ganin hukumomin na Najeriya na jan kafa kan lamarin.