Ma’aikatan sun bayyana cewa, gwamnatin Jamhuriyar Nijar bata dauki kananan ma’aikata da muhimmanci ba, ta haka bata kulawa da wahala da kuma bukatunsu, suka kuma ci alwashin ci gaba da tursasawan gwamnati har sai sun sami biyan bukata.
Babban magatakardar hadakar kungiyar kananan ma’aikatan Kamarat Gagara Tasau ya bayyana cewa, kananan ma’aikata basu cin moriyar duk wani aikin da gwamnati ke yi na kyautata rayuwar ma’aikata da ya hada da gidaje da kuma taimakon jinyar likita idan su, ko iyalansu basu da lafiya.
Wakilinmu Abdoulaye Mamman Amadou ya bayyana cewa, ma’aitan sun shiga yajin aikin ne a daidai lokacin da majalisar ministoci take zama.