Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Gida Daya Duk Sun Mutu A Wani Hadarin Jirgin Sama


Wurin da jirgin ya fadi
Wurin da jirgin ya fadi

Wani jirgin sama me dauke da Amurkawa ya fado kuma ya kone inda yai sanadiyyar mutuwar gabaki daya wanda yake dauke dasu.

Jami'an kasar Costa Rica sunce suna binciken sanadin faduwar jirgin saman da ta wakana jiya Lahadi, a wani yanki mai duwatsu da bishiyoyi wanda ke yamma da birnin San Jose. Amurkawa su 10 dake cikin jirgin tare da matukansa su biyu sun mutu a wannan hatsari.

Jami'ai sunce jirgin, mallakar wani kamfanin safarar jiragen saman kasar mai suna Nature Air, ya kama da wuta a lokacin da ya fado. Babu wanda ya tsira da rai a cikin jirgin.

Wata dake zaune a bayangarin birnin New York, ta ce 5 daga cikin wadanda ke cikin jirgin 'Yan gida daya ne kuma hutu suka tafi. Ta ce 'yan'uwan nata da suka hallaka a wannan hatsari sune Bruce da Irene Steinberg da 'yayan su maza uku Matthew, William da Zachary dukkansu mazauna garin Scarsdale.

'Yar'uwar ta Bruce, Tamara Steninberg Jacobson, tayi amfani da shafin facebook indata dora hotunan su ta kuma bayyana cewa suna cikin dimauta da jimami.

A lokacin da yake magana da manema labarai, Darektan kula da harkokin zirga zirgar jiragen saman farar hula na Costa Rica, Enio Cubillo, yace jirgin da akai shata na Nature Air ya tashi ne da tsakar rana jiya lahadi daga Punta Islita inda ya kama hanyar San Jose a lokacin da ya fado, ya kuma bayyana sunan matukin jirgin Juan Manuel Retana a matsayin kwararre, kuma suna ci gaba da binciken dalilin hadarin. Shugaban kasar Costa Rica Luis Guillermo yace gwamnatin sa ta yi tsannanin nadama akan faruwar lamarin

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG