Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AMURKA: Sojojin Ruwanta Sun Soma Raka Jiragen Ruwan 'Yan Kasuwa


Mashigin ruwan Hormuz inda jiragen ruwa ke ratsawa
Mashigin ruwan Hormuz inda jiragen ruwa ke ratsawa

A wani yunkurin mayarda martani bisa ga yadda Iran ta tsare wani jirgin ruwa a tekun Fasha Amurka ta soma raka duk jirgin ruwan 'yan kasuwa dake da tutarta da zai ratsa cikin tekun Fasha ko tekun Larabawa

Sojojin ruwan Amurka sun fara raka duk jiragen ‘yan kasuwa da suke ‘dauke da tutar Amurka har zuwa mashigar ruwan Hormuz daga bakin kogin Fasha, domin tabbatar da cewa Iran bata yi musu katsalandan ba.

Jami’an ma’aikatar tsaron Amurka sunce, an dauki wannan matakin ne a zaman martani kan abunda hukumomi da suke Washington DC suka kira takala daga Iran. Farkon satin nan ne dai aka sami rahotan cewa jiragen yaki na ruwa daga Iran sunyi harbin gargadi a kusa da jirgin ruwa mai dakon kaya wanda yake dauke da tutar tsibirin da ake kira Marshall Sukatsare kuma ta kama jirgin da ma’aikatansa.

Iran dai tace ta kama jirgin Maersk Tigris din ne saboda tana bin kamfanin daya mallaki jirgin kudi, a wani hukunci da kotu ta bata.

Ya yinda sojojin ruwan Amurka sukecigaba da kasancewa a tekun Fasha da tekun arewacin Arabiya, wannan sabon yunkurin a fili ya bukaci jirgin yakin Amurka ya zamanto kan hanyar dake tsakanin Iran da Oman a lokacin da duk wani jirgin ‘yan kasuwa na Amurka ke ratsawa ta ruwan.

A karkashin dokar kasa da kasa, jiragen ruwa nada ikon wucewa ba tare da an tsayar dasu ba, muddin basu sabawa dokar hana jigilar makamai ko su gudanar da ayyukan leken asiri.

XS
SM
MD
LG