Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban reshen matasan jam'iyar ANC zai san makomarshi


Shugaban kungiyar matasan jam'iyar ANC, Julius Malema
Shugaban kungiyar matasan jam'iyar ANC, Julius Malema

Yau shugaban matasan Afrika ta Kudu na jam’iyar African National Congress Julius Malema , zai san makomar shi a jam'iyar

Yau shugaban matasan Afrika ta Kudu na jam’iyar African National Congress –ANC da ruwa siyasa ke neman hadiyewa, zai san makomar shi kan ko kalubalantar dakatar da shi da jam’yar tayi ta zauni ko babu.

Kwamitin ladabtarwa na jam’iyar ANC zai sanar da shawarar da ya yanke yau kan neman ahuwar da Julius Malema ya yi a kan dakatar da shi da jam’iyar tayi na tsawon shekaru biyar sabili da kokarin rarraba kawunan ‘yan jam’iyar da yayi.

A shekarar da ta gabata ne jami’an jam’iyar suka sami Malema da wadansu shugabannin matasa hudu da laifin shuka gaba da tsatsaguwa tsakanin ‘yan jam’iyar.

Sauran shugabannin ma suna kalubalantar hukumcin da cewa, ba a basu damar kare kansu ba kafin jam’iyar ta yanke hukumcin.

Idan jam’iyar bata saurare su ba, yana yiwuwa Malema da sauran abokanshi su kai kara kotu.

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG