Najeriya da Afirka ta Kudu sunce shugaban Amurka ne ya bukaci tattaunawar, wanda ya zuwa yanzu bai ce komai ba game da wata kasa a nahiyar Afirka ko matsalolinsu, tun lokacin da ya hau karagar mulki.
Fadar shugaban Najeriya tace Trump da Buhari sun tattauna kan batun yaki da ta’addanci, kuma Trump ya tabbatarwa da Buhari cewa Amurka a shirye take wajen samar da wata sabuwar yajejeniya ta taimakawa da Najeriya, musamman ta fannin kayan yaki.
Haka kuma Trump ya jinjinawa Buhari game da kokarin da Najeriya ta ke na yaki ‘yan tsagerun kungiyar Boko Haram, ya kuma gayyaci Buhari da ya zo Washington a duk lokacin da ya shirya.
Shugaba Mohammadu Buhari bai fito bainar jama’a ba tun lokacin da ya tafi London domin a duba lafiyarsa ranar 19 ga watan Janairu.