Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Kashe Dala Miliyan 10 Don Dakile Yaduwar Murar Tsuntsaye


Wani gidan kaji a Amurka
Wani gidan kaji a Amurka

Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Yaduwa ta Amurka ta fada a ranar Talata cewa, tana shirin kashe dala miliyan 10 don dakile kamuwa da cutar murar tsuntsaye tsakanin ma’aikatan gona, da ya hada da dala miliyan 5 don rigakafin mura na lokaci-lokaci.

Wannan yunkurin wani bangare ne na kokarin da take na kaucewa ci gaba da yaduwa da rikedewar kwayar cutar.

Barkewar cutar murar tsuntsaye da ke ci gaba da kama garken kaji a kusan kowace jihar Amurka tun daga shekarar 2022, da kuma shannu samar da madara sama da 170 a jihohi 13 tun daga watan Maris, a cewar Ma'aikatar Aikin Gona ta Amurka.

Ma'aikatan kiwon kaji da masu kiwon dabbobi 13 sun kamu da kwayar cutar a Colorado, Michigan da Texas, a cewar CDC. An gano tara daga cikin wadanda suka kamu da cutar a watan Yuli a tsakanin ma’aikatan da ke yanka kaji a wasu gonakin kaji guda biyu masu dauke da murar tsuntsaye a Colorado.

Shanu a wata gona a New Vienna, Iowa
Shanu a wata gona a New Vienna, Iowa

Har yanzu jama’a basu cikin hadarin kamuwa da murar tsuntsaye, in ji babban darektan CDC Nirav Shah a wata kira da manema labarai suka yi da shi.

Hukumar da ke Atlanta za ta ware dala miliyan 5 ga kungiyoyi da suka hada da Cibiyar Kula da Lafiyar Ma’aikata ta Kasa don ilimantar da horar da ma’aikata kan kare kansu daga kamuwa da murar tsuntsaye, da kuma wani dala miliyan 5 don samar da allurar rigakafin mura ga ma’aikatan gona, in ji Shah.

Shah ya kara da cewa, duk da cewa maganin mura na lokaci-lokaci ba ya bayar da kariya daga kamuwa da cutar murar tsuntsaye, amma tura allurar rigakafin na iya rage wa ma’aikata hadarin kamuwa da mura da yanayi ke haifarwa da kuma murar tsuntsaye a lokaci guda, wanda zai iya haifar da sauye-sauyen kwayar cutar mura, in ji Shah.

Allurar rigakafin murar tsuntsaye
Allurar rigakafin murar tsuntsaye

"Magance kamuwa da mura na lokaci-lokaci ga waɗannan ma'aikata, wadanda da yawa daga cikinsu kuma suna kamuwa da murar tsuntsaye, na iya rage hadarin sabbin nau'ikan mura da ke fitowa," in ji Shah.

Shah ya kara da cewa, CDC na fatan yiwa daukacin ma'aikatan kiwon dabbobi kusan 200,000 allurar rigakafin cutar mura ta bana, kuma tana aiki tare da jihohi don samar da tsare-tsare na isa ga ma'aikatan.

USDA ta yi imanin cewa, za ta iya dakatar da yaduwar cutar murar tsuntsaye a tsakanin shanun kiwo kuma a karshe za ta kawar da cutar, in ji Eric Deeble, wani karamin sakatare na hukumar.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG