Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Hana Wasu 'Yan Ghana Biza


Shugaban Ghana Nana Addo da Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala a Harris yayin wata ziyara da Nana Addo ya kai Amurka a shekarar 2021
Shugaban Ghana Nana Addo da Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala a Harris yayin wata ziyara da Nana Addo ya kai Amurka a shekarar 2021

Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da Ghana ke shirin gudanar da zaben shugaban kasa a watan Disambar 2024.

Amurka ta sanar da wani tsarin takaita biza ga mutanen da hukumomin Washington ke ganin suna da alhakin haifar da cikas ga tsarin dimokradiyya a Ghana, gabanin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin kasar da za a gudanar a watan Disamba a kasar wacce ke Yammacin Afirka.

"Wannan tsarin takaita biza zai shafi wasu mutanen da ke cin dunduniyar tsarin dimokradiyya ne kawai kuma ba ana nufin za ta shafi al’ummar Ghana ba ko kuma gwamnatin Ghana," in ji Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken a wata sanarwa da ofishinsa ya fitar a ranar Litinin.

Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da Ghana ke shirin gudanar da zaben shugaban kasa a watan Disambar 2024.

Amurka kan yi amfani da tsarin takaita biza a matsayin hanya ta hukunta wasu manyan mutane da za su iya kasancewa masu zaman kansu ko jami’an gwamnati a kasashe da dama.

A cewar sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen ta fitar, Amurka ta kuduri aniyyar tallafawa da inganta dimokradiyya a Ghana da ma duk duniya baki daya.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG