Wannan aiki da jaridar Washington Post ta fara rawaitowa, yana auna iyalai dubu biyu a manyan biranen Amurka inda galibin bakin haure ke zama, kamar su Houston, Chicago, Miami da Los Angeles. Jaridar Post tace ta samu bayanin samamen da za a kaiwa bakin haure ne a wurin wasu jami’an Amurka guda uku da suka nemi a sakaya sunayen su.
Ita kuwa jaridar The Miami Herald ta ambato wasu birane da za a gudanar da kamen da suka hada da Atlanta, Baltimore, Denver, New Orleans, New York da kuma San Francisco.
Trump ya aike da wani sakon Twitter a ranar Litinin cewa Amurka zata fara korar miliyoyin bakin haure da basu da iznin zaman kasar daga mako mai zuwa, amma kuma sai wannan sanarwar tazo ma jami’an migireshin da al’ajabi.
Jami’an gwamnati sun ce an yanke shawarar korar bakin hauren da basu da iznin zama watanni da dama amma kuma jami’an migireshin sun ce ya zuwa farkon wannan mako babu wani batu kamar haka.
Facebook Forum