Mai bada shawara akan sha’anin tsaro na fadar Amurka ta White House Robert O’Brien, ya ce ba zai so ya yi hasashe ba akan kasar Koriya ta Arewa da barazana ta “kyautar Kirsimeti”, amma ya ce Amurka za ta damu, idan Pyongyang ta yi gwajin makamin nukiliya mai cin dogon zango.
A wata tattaunawa da kafar yada labarai ta ABC, O’Brien ya ce kasar za ta dauki matakan da suka dace a matsayin ta na jagorar kasashe da suka fi karfin soji da na tattalin arziki, idan har Koriya ta Arewa ta ci gaba da yin gwajin.
O’Brien ya kara da cewa Amurka tana da hanyoyi da dama na maida martani.
Koriya ta Arewa ta yi gargadin ba da “kyautar Kirsimeti” muddin Amurka ba ta cika wa’adin nan da karshen shekara ba, na sassautowa daga matsayar ta akan tattaunawar nukiliya, wadda ke kwan-gaba kwan-baya tun daga watan Fabrairu.
Jami’an Amurka na cikin shirin ko ta kwana akan yiwuwar gwajin makamin nukiliya mai cin nisan zango, tun sa’adda Koriya ta Arewa ta ba da gargadin.
Duk da yake hutun kirsimeti ya wuce Koriya ta Arewa ba ta yi abin da ta kira kyautar ta kirsimeti ga Amurka ba, dangantakar kasashen biyu na kara kasancewa abu mai wuyar sasantawa.
Tattaunawa akan warware makamin nukiliyar kasar Koriya ta Arewa ya shige bacci, tun sa’adda taro na 2 tsakanin shugaba Trump da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un bai sami nasara ba a farkon wannan shekara.
Facebook Forum